
Fadar shugaban kasa tace gwamnatin shugaba Buhari ya cancanci yabo sakamakon rage rashawa a cikin jama’a kuma zata cigaba da taimakawa a bangaren wayar da kai na ayyukan hukumomi kan rashawa.
Mai magana da yawun shugaban kasa Mallam Garba Shehu shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa yayin da yake magana kan rahoton ayyukan rashawa a Najeriya.
Rahoton shekarar 2020 wanda Transparency International ta fitar, ta bayyana Najeriya ta samu kaso 25 cikin maki 100 wanda take mataki na dari 1 da 49 cikin kasashe dari 1 da 80.

Rahoton ya cigaba da zargin kasar Najeriya ta cewa ta kasance kasa na biyu a bangaren rashawa a yankin Afrika ta kudu bayan kasar Guinea Bissau da ta kasance kan gaba a bangaren rashawa a yankin.
