Duniya Tayi Bikin Ranar Radiyo Na Sàhekarar 2021 .

radio-studio-1.jpg
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By:Babagana Bukar Wakil, Maiduguri
An bayyana ranar 13 ga watan Fabrairun kowace shekara a matsayin ranar radiyo ta duniya da haka kuma an samar da ayyukan watsa labarai na kasa da kasa na majalisar dinkin duniya a ranar 13 ga watan nan a shekarar dubu 1 da dari 9 da 4 da 6.

Ranar radiyo ta duniya na wannan shekara mai taken TARIHI.

Radiyo hanya ce na isar da sako cikin sauki kuma wanda aka yarda da shi.
Yayin da suke bayyana ra’ayin su game da ranar Mal. Muktar Alkali wani dan jarida yace radiyo yana canza rayuwar mutuum baki daya.

Aisha Musa wata karamar yar kasuwa tace idan babu radiyo kunnuwan su baya samun cikakken labarin abinda yake faruwa a duniya.

Aysha tace radiyo wani bangare na jikin su ne da bazasu iya rabuwa da shi ba kuma yana koyar da su kan tattaunawar sulhu, hakuri da zaman lafiya.

Daya daga cikin masu tace labarai na gidan radiyo Dandal Kura Hadiza Garba ta bayyana cewa radiyo na da karfi badan abin magana bas ai dan wanda yake maganan.

Shugabar sashin shirye shirye na gidan radiyo Dandal Kura Hajiya Fatima Ibrahim Mu’azzam ta bayyana cewa radiyo na bada wata daman a inganta alaka tsakanin jama’a ta hanyar damawa a kafafen sada zumunta da gidajen radiyo.

Wani wakilin jaridar Blue print Alh. Sadiq Abubakar yayi kira ga jama’a da su hada hannu kan yancin magana domin daraja ranar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply