
Ministan kiwon lafiya Dr Osagie Ehanire yace kasar Najeriya zata iya samun rigakafin cutar COVID-19 a watan janairu shekarrar 2021 idan ba’a dakatar da aiki da akeyi akai ba.
Ehanire ya bayyana hakkan ne bayyan fitowa daga taron su da majalisar zartarwa a fadan shugaban kasa.
Ya kuma kara da cewa kasashen da suka kirkiri rigakafin zasu fara yiwa al’ummarsu rigakafin kafun ya iso saura kasashen, kuma yace aiki da hukumar lafiya ta duniya zai sa a samu kigakafin a kan lokaci.

Ehanire yace kasar najeriya zata samu rigakafi mafi sauki adanawa.
