Dr Gabriel Ya Yabawa Kokarin Shugaba Buhari Wajen Yakar Rashin Tsaro A Kasar

images (45)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kungiyoyi masu zaman kansu na Najeriya Dr Nwambu Gabriel wanda yayi jawabi a madadin dukkan kungiyoyin ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa kungiyar ta kammala taron ta na kwana daya game da matsalar rashin tsaron najeriya.

Dr Gabriel ya yabawa kokarin shugaba Muhammadu Buhari wajen yakar rashin tsaro tare da cewa goyon baya daga ministocin sa kadai yake bukata
Ya ce a yanzu kungiyar Boko Haram tana da reshe da dama wanda ya zama sanadiyyar ta’addanci tsakanin kasashe, yan bindiga, da masu fyade, harda masu satan shanaye, yan garkuwa da mutane da sauran su wanda yace tabbas yan siyasa nada kaso cikin abinda yake faruwa a kasar

Ya bukaci majalisar dattawa dasu cire shuwagabannin wadanda suka gaza su sauya su da wasu daban masu tsoron ubangiji domin samun zaman lafiya, tsaro da kuma ci gaban kasar daidai da muradin shugaban kasa

Mr Gabriel ya kuma ce majalisar ta amince da ayyukan shuwagabannin tsaron bisa ayyukan da sukayi na fuskantar matsalolin tsaron kasar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply