Daular larabawa ta dagewa wasu kasashe hukunscin shiga kasarsu

Hadin gwiwar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a Dubai sun sanar da yin garambawul a cikin hanyoyin matafiya da ke zuwa daga Jamhuriyar Indiya, Afirka ta Kudu da Najeriya a ranar 19 ga Yuni.

Wata sanarwa daga Ofishin Yada Labarai na Ofishin Jakadancin Hadaddiyar Daular Larabawa da ke Abuja a ranar Lahadi ya bayyana cewa sabbin dokokin da Kwamitin Koli na Rikici da Bala’i ya bayar a Dubai zai fara aiki ne daga ranar 23 ga Yuni, a cewar sanarwar ta Shugaban Kwamitin Koli, Sheikh Mansoor Al-Maktoum ya fitar.

Sunce hakan zai kare fasinjoji da sauƙaƙa musu matsaloli ba tare da yin lahani ga matakan rigakafin COVID-19 ba.
Sanarwar Ofishin Watsa Labarai ta ce wani bangare ne na tsari na yau da kullun na bita da inganta matakan rigakafi dangane da sabbin ci gaban cikin gida, yanki da na duniya.

Bayan sanarwar, kamfanin jirgin saman UAE na Emirates ya tabbatar da cewa zai fara jigilar fasinjoji daga Afirka ta Kudu, Najeriya da Indiya bisa ga sabbin ka’idojin daga ranar 23 ga watan Yuni.

Ya kuma ce masu takardar izinin ta visa daga Indiya da kuma matafiya daga Afirka ta Kudu ya kamata su dauki allurai biyu na rigakafi kamar yadda da hukumomin daular larabawan suka amince da kuma rahotanni na gwajin daga ɗakunan gwaje-gwajen da gwamnatocin tarayya na ƙasashe suka amince da su.

Amma ga ‘yan Najeriya ba dole sai sunyi allurar ba amma duk wasu sharuɗɗa suna aiki.