Dakarun sojojin Chadi Dana Kamaru Sun Hada Hannu Domin Yakar Yan Ta’adda A Yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya.

MNJTF 2
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar hadin gwiwa na sojoji daga kasashen Chadi da Kamaru sun iso jihar Borno domin taimakawa wajen yaki da yan ta’adda a yankin arewa maso gabashin kasar nan da yankin tabkin Chadi.

Tun shekarar 2009 kungiyar Boko Haram ta sanadiyyan mutuwar mutane sama da dubu 30 sannan sama da mutane miliyan 2 sun rasa matsugunan su a yankin.

Gidan radiyo Dandal Kura ta rawaito cewa zuwan jami’an hadin guiwar dauke da makamai zai karfafa kokarin rundunar sojojin Najeriya dake aiki a dajin Alagarno da Timbuktu.

Shirin operation Tura Takai Bango wanda ke aiki karkashin shirin operation Lafiya Dole, tana aiki ne musamman a lokacin rani da kayakin aiki da suka hada da motocin yaki dauke da bindigogi.
The z

A na sa ran rundunar hadin guiwar zasu karfafawa jami’an tsaron Najeriya a yankin arewa, kudu da kuma Borno ta tsakiya.

Gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum a shekarar 2020 ya bukaci gwamantin tarayya da ta nemi taimakon kasashe makwabta musamman gwamnatin Chadi, Kamaru da jamhuriyar Nijar wajen kakkabe yan ta’addan Boko Haram a mabuyar su.

Tuni kasashen Chadi, Najeriya, Nijar Kamaru da kuma Benin sun tura jami’an su da kayakin aiki zuwa shalkwatan rundunar hadin guiwa dake N’Djamena da kuma shalkwatan shiyyoyi a Bagasola a Chadi, Baga a Najeriya, Diffa a Njiar sai kuma Mora a Kamaru.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply