Dakarun Sojoji Sun Kashe Yan Ta’adda Da Dama Tare Da Lalata Wajen Taron Su, A Jihar Yobe.

scene-of-nigerian-ground-troops-that-recapture-baga-4
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar sojojin Najeriya tace jami’an ta karkashin shirin operation Tura Takai Bango sun kashe yan kungiyar Boko Haram dana ISWAP a wajen taron a kauyen Bayamari na jihar Yobe.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar birgediya janar Muhammad Yerima shi ya bayyana haka a garin Abuja.

Yace jami’ai karkashin shirin operation Lafiya Dole suna cigaba da tarwatsa yan ta’addan a yankin arewa maso gabas.

Yace dakarun runduna na 159 dana bataliya 233 tare da hadin guiwar jami’an sa kai na CJTF bayan samun bayanan sirri sun kai hari gay an ta’addan a Bayamari.

Yace jami’an sojojin sun kwato bindigar AK 47 da alburushi.

Ya kara dacewa yawan nasarorin da ake samu akan yan ta’addan Boko Haram dana ISWAP a mabuyar su ya nuna cewa an kusa a kawar da su a yankin arewa maso gabas baki daya.

Daga karshe an yaba da kokarin jami’an operation Tura Takai Bango na kawar da yan ta’addan daga mabuyar su da sukeyi.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply