cibiyar lafiya matakin farko na jihar Adamawa tare da hadin kan kungiyar tallafawa asusun yara kanana na UNICEF tace zata horas da iyaye mata dubu 6 da 255 game da sa ido kan sanya ido a matakin ciyarwa na abinci mai gina jiki na ya’yansu jami’in UNICEF a Najeriya Martins Ladu ne ya bayyana hakan yayin taron sakatarorin kananan hukumomi da ma’aikatan abinci na bangaren a birnin Yola litinin yace horas da ma’aikatan zai taimaka wa tsare-tsaren aikin inda yace kungiyar UKAid ne ta bada tallafin ta UNICEF wanda ake sa ran za’a aiwatar ta a kananan hukumomi 21 na jihar Adamawa. Babban ma’aikacin hukumar a jihar Bauchi Tushar Rene, yace makasudin shirin shine karfafa mata, iyalai sa kuma masu bada kula ga lafiyar yara kanana domin sanin matakin cimaka na ya’yan su, saurin gano matsala dama magance cutar tamuwa duba da yadda akeci gaba da samun matsalolin.. shugaban ADPHCDA Dr Suleiman Bashir, ya yabawa UNICEF dama sauran abokan cigaban da suka kai 10 bisa irin goyon baya da suke bayarwa na ceto yara kanana sannan yace gwamnatin jihar ta dukufa wajen tabbatar da cewa an samu nasarar shirin ceton yara daga cutar na Tamuwa..

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

cibiyar lafiya matakin farko na jihar Adamawa tare da hadin kan kungiyar tallafawa asusun yara kanana na UNICEF tace zata horas da iyaye mata dubu 6 da 255 game da sa ido kan sanya ido a matakin ciyarwa na abinci mai gina jiki na ya’yansu.

jami’in UNICEF a Najeriya Martins Ladu ne ya bayyana hakan yayin taron sakatarorin kananan hukumomi da ma’aikatan abinci na bangaren a birnin Yola litinin

yace horas da ma’aikatan zai taimaka wa tsare-tsaren aikin inda yace kungiyar UKAid ne ta bada tallafin ta UNICEF wanda ake sa ran za’a aiwatar ta a kananan hukumomi 21 na jihar Adamawa.

Babban ma’aikacin hukumar a jihar Bauchi Tushar Rene, yace makasudin shirin shine karfafa mata, iyalai sa kuma masu bada kula ga lafiyar yara kanana domin sanin matakin cimaka na ya’yan su, saurin gano matsala dama magance cutar tamuwa duba da yadda akeci gaba da samun matsalolin.

shugaban ADPHCDA Dr Suleiman Bashir, ya yabawa UNICEF dama sauran abokan cigaban da suka kai 10 bisa irin goyon baya da suke bayarwa na ceto yara kanana sannan yace gwamnatin jihar ta dukufa wajen tabbatar da cewa an samu nasarar shirin ceton yara daga cutar na Tamuwa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Related stories

Leave a Reply