Cibiyar Bada Agaji Ta Sarki Salman Ta Bada Kayan Abinci GA ‘Yan Gudun Hijira 3972

From Hadiza Garba, Maiduguri
Cibiyar bada agaji ta Sarkin Salman ta bada kayan agaji inda aka kaddamar da rabon kayan abincin ga magidanta ‘Yan Gudun Hijira 3972.

Mataimakin jakadan masarautar Saudi Arabiya Ibrahim Alghamedi, Ministan Affaos na Jin kai da Kula da iftila’i ya sami wakilcin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan kungiyoyi masu zaman kansu da kula da iftila’i Alhaji Musa Bungudu.

Wakilin Darakta Janar na NEMA Hajia Fatima Kazim da mai kula da shiyyar NEMA ta Arewa maso Gabas Wagami Lydia Madu sun kasance wajen gabatar da kayayyakin ga wadanda suka amfana.

Darakta Janar BOSEMA Hajiya Yabawa Kolo ta yaba da wannan tallafi da masarautar Saudiyya ta yi musu.

Kayan da aka bayar sun hada da Shinkafa, Wake, masavita man gyada, kayan kamshi, tumatir da gishiri.