CAN Ta Bukaci Mabiya Addinin Krista Dasu Kula Da Dokokin Kare Kai Na COVID-19

CAN small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar mabiya addinin Krista na Najeriya CAN ta bukaci mabiya addini Krista das u kula da dokokin kariya na COVID-19 a wannan lokaci da bikin kirsimeti ke gabatowa.

Daraktan al’amura na kungiyar shiyyar jihar Kwara Mr Shona Ibiyemi ne yayi tsokacin yayin tattaunawa day an jaridu a Ilorin.

Yace a wannan lokaci da kasar take fuskanta karuwar cutar karo na biyu, ana bukatan jama’a su kula tare da kare kansu ta hanyar amfani da takunkumin fuska da kuma bada tazara kuma ya bukaci dukkan bajami’o’I su kasance sun bada wadatacciyar fili da kuma na’urar auna mutum,.
har ila yau kungiyar tayi kira ga gwamnonin jihohi dasu dada wayar da kan mata yan’kasuwa musamman da kuma direbobin haya dana machine game da kula da dokokin kariyar duk da pasinjojin su.

Yace kungiyar tana iya kokarinta na fadakarwa a bajami’u game da cutar sannan sun nemi gwamnatin jihar Kwara da a kafa doka wanda za’a tabbatar da cewa jama’a sunyi amfani da dokokin na kariya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply