Buratai Yayi Kira Ga Manyan Sojoji Dasu Kara Kaimi A Ayyukansu.

Buratai-middle-in-Borno
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hafsin sojojin kasa laftanar janar Tukur Buratai ya kirayi manyan sojijin da su kara kaimi a ayyukansu tare da dukufa wajen yin addu’oi na mussanman domin yaki da rashin tsaro.

Buratai yana wannan bayani ne a wajen taron Karin masayi da akayiwa sojoji zuwa matsayin manjo janar,Yace sojoji sun shirya wannan taron tunatarwar domin neman taimakon Ubangiji a yayin da suke yaki a filin daga.

Yace ansamu taimakon Ubangiji a yayin zanga-zangar EndSARS inda domin ba’ayi rasa rayuka ba a Lekki Tollgate dake jihar lagas.

Yace za su cigaba da kare dukkan yayan kasa masu bin doka.

Gidan Radiyo Dandal Kura Radio International ya bayyana cewa Ahmed Taiwo jami’i dake sashin lekan asiri na sojin da yakare sojin kasar a game da zanga-zangar EndSARS yana daya daga cikin wadan da aka karawa matsayi.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply