Buhari ya zanta game da aikin layin jirgin kasa na Kano, Katsina,Jibya zuwa Maradi

Buhari
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci ma’aikatun tafiye-tafiye da na kudi dasu kammala yerjejeniyar kudade da ake bukata da wadanda zasu hada kai da gwamnati domin gina layin jirgin kasa daga jihar Lagos zuwa Calabar hade da manyan biranai a yankin kudu maso gabas da kudu maso kudancin kasar.

Shugaba Buhari yaba da wannan umarni ne yayin bikin samar da hanyar jirgin kasar daya hada da jihar Kano zuwa Katsina, Jibiya da Maradi na jamhuriyyar Nijar.

Ya kara da cewa layin jirgin kasar zai hada biranen yamma maso gabas na kasar da suka hada da Onitsha, Benin, Warri, Yenegoa, Port Harcourt, Aba da Uyo kuma yace tuni an rattaba hannu kan yerjejeniyar layin jirgin kasar zuwa Itakpe zuwa Baro da zai hade Abuja da Lokoja sanna yace an rattaba hannu kan shirin samar da tashar jirgin ruwa a Warri kuma yanasa ran za’a kammala shi cikin wa’adin gwamnatin sa.

Daya jawabi game da layin jrigin kasar na Kano zuwa Maradi yace hakika zai kawo sauki wajen kasauwanci tsakanin Najeriya da Nijar kuma zai bada damar kutsawa yankunan arewa da kudancin kasar hade da sauki ga tafiyen-tafiyen pasinjoji da kuma sauki wajen shigo da amfanin albarkatu, musamman ma amfanin noma ga kasashen biyu.

Daga karshe shugaba Buhari ya yabawa kamfanin Messrs Mota-Engil bisa kokarinta da shigowa da kayan zamani a aikin.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply