Buhari Ya Zabi Olonisakin, Buratai, Abubakar , Usman A Matsayin Jakadu

Buhari
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya mika sunanyen tsofaffin shugabannin tsaro da aka sauke ga majalisar dattijai don amincewarsu a matsayin jakadu na musamman.

Hakan na cikin takardar da babban mai bawa shugaban kasar shawara kan harkar yada labarai da hulda da jama’a Femi Adesina ya fitar a jiya.

Rahoton yace shugaban kasar ya tura takarda ga shugaban majalisar dattijai Sanata Ahmad Ibrahim Lawan inda shugaban kasar yace kamar yadda yake a kundin tsarin mulki a sashi na 171 (1), (2) (c) da kuma sashin kasa na (4) na kundun tsarin mulkin shekarar 1999 na kasar ta Najeriya da aka gyara inda shugaban yace ya mika sunayen mutanen 5 a matsayin jakadu na musamman.

Mutanen sune mai ritaya Gen Abayomi G. Olonisakin , mai ritaya Lt Gen Tukur Y. Buratai, mai ritaya Vice Admiral Ibok-Ete Ibas, mai ritaya Air Marshal Sadique Abubakar da mai ritaya Air Vice Marshal Mohammed S. Usman.

Haka nan a rahoton shugaban kasar ya bukaci yan majalisar dasu gudanar da aikin cikin gaggawa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply