
Kimanin sojoji 8 ne suka rasu 3 kuma suka bata bayanda yan kungiyar Boko Haram suka kai hari matsugunin sojoji dake Arewa maso gabashin yankin Difa dake Nijar kamar yadda shugaban rundunar tsaron kasar ya tabbatar.
Yayin da yake Magana da manema labarai Issoufou Katambe yace yan kungiyar ta Boko Haram sun tunkari matsunin sojojin na Chetima Wongou dake yankin Diffa da jerin gwanon motoci 20 dauke da maggan makamai.
Katambe ya kara da cewa rundunar sojin kasar sun kwace mota guda daya, sun lalata wata inda jami’an hadin giwa na Multinational Joint Task Force suka harbi ragowar inda daga nan suka gudu zuwa iyakar Najeriya.

Diffa dai ta dade cikin dokar t abaci fiye da shekaru 5 tun bayan da Boko Haram lsuka kaiwa jami’an tsaro hari watan Fabarairu na shekarar 2015.
