Najeriya: Babu Wani Gari Dake Karkashin Ikon Boko Haram- Shehun Borno

shehu
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Mai martaba shehun borno Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai El Kanemi ya bayyana cewa babu wani gari dake karkashin kulawan yan kungiyar boko haram a cikin jihar Borno.

Mai martaban ya kuma bayyaan jin dadinsa, dangane da komawar da yan gudun hijirar jihar suka farayi zuwa garuruwarsu.

El kanemi ya kuma kara da cewa, tuni yan gudun hijirar kananan hukumomin Kala balge, Abadam, Guzamala, da kuma Marte suka koma garuruwansu suka rungumi noma da kiwo.

Shehun yayi wannan jawabinne a lokacin da ya kai ziyara gidan gwamnatin jahar borno.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, gwamna Kashim Shettaima ya jinjinawa shehun danga ne da wannan ziyarar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply