Babban Sufetan Yan Sandan Muhammad Adamu Ya Kai Ziyara Jihar Katsina.

POLICE-IG-ADAMU
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Cikin wani ziyara da Sufetan yan sandan kasa Muhammad Adamu yakai jihar Katsina yace fararen hula 51 ne aka kashe, yan sanda kuma 22 yayin zanga-zangar End SARS.

Sufetan yace rundunar yan sanda zatayi aiki da masu ruwa da tsaki, ciki harda kungiyar makiyaya Fulani na Miyetti Allah dama sauran kungiyoyin domin bullo da sabbin hanyoyin hana ayyukan yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Ya kuma ce baza’a kuma samun makamancin garkuwa da daliban makarantar gwamnati da akayi a jihar Katsina ba kwanaki inda yace yan sanda ne keda nauyin tabbatar da bada kariya a cikin gida kuma a saboda haka ba zasu baiwa mabarnata dama ba.

Yayin ziyarar sufetan yan sandar ya gana da ma’aikatan cibiyar da kuma komandojin shiyyar duk akan batun samar da tsaro a jihar Katsina.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply