Babban Hafsan Rundunar Tsaron Kasa Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai Ya Bukaci Sabbin Sojoji Da Aka Dauka aiki Da Su Shirya Tsare Kasar Su .

Chief-of-Army-Staff-Major-General-T-Y-Buratai
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Babban hafsan rundunar tsaron kasa laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ya bukaci wadan da aka dauka aiki da su shirya tsare kasar su kan duk wani nau’I na barazana.

Yayi wannan kiran ne lokacin da ake tantancewar karshe na wadan da aka dauka aiki karo na 80 da akayi a dajin Falgore dake karamar hukumar Tudun Wada na jihar Kano.

Haka kuma yayi kira a gare su da su shirya zuwa dajin Sambisa inda ya kasance mabuyar yan kungiyar Boko Haram a jihar Borno.

Ya kara dacewa ya kamata su san cewa kasar su zasuyi wa hidima, kuma yayi kira a gare su da su kasance masu biyayya, daga karshe yace nan gaba a dajin Falgore za a fara tantacewa da daukan aiki kuma yayi kira da su zama masu hazaka da jajircewa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply