
Banban bankin kasar CBN ta kwace lasisin na kanannan Bankuna 42.
Kamfanin inshorar Najeriya ne ta bayyana hakkan a shafinta.
Kamfanin inshorar, wanda itace lura da al’amuran bankunan tace zata kulle wadannan bankuna da aka lissafo kuma ta maidawa wadanda suke da hannun jari kudadensu.

Da hakkan ta bukaci dukkan wadanda suke da kudi a wadannan bankuna da su ziyarci wadannan bankuna da aka rufe kuma su garzaya Kamfanin inshore ta kasa domin karban kudadensu.
Kamfanin ta bada jerin sunayen bankuna 42 da aka rufe.
