Babban Alkali A Jihar Katsina Yace Daliban Da Ake Yayewa Yanzu Da Na Da Azkwai Banbanci Ta Bangaren Dabi’u Da Sauran Su.

katsina 2
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Babban alkali na jihar Katsina mai shari’a Musa Danladi Abubakar yace daliban da ake yayewa yanzu da na da baya akwai banbanci ta bangaren dabi’u da sauran halaye.

Yace halayen daliban na yanzu ba zai sanya su kasancewa shuwagabanni na kwarai ba domin suna karancin dabi’u na kwarai.

Ya bayyana haka ne a wajen taron da shugaban kungiyar manoma ta kasa Kabir Faskari ya shirya a madadin daliban shekarar dubu 1 da dari 9 da 72 zuwa 76 na makarantar sakandaren gwamnati a Katsina.

Gwamnan jihar Aminu Bello Masari na jihar Katsina yace ta kamata tsoffin daliban su na ziyartar tsoffin makarantun su domin bada kwarin guiwa ga daliban.

Yayi kira ga masu hannu da shuni da dai daikon jama’a da suyi taimaka wajen samar da cigaba a makarantu, daga karshe wanda ya shirya taron Kabir Ibrahim yace tsoffin daliban zasu samar da wani hanyar cigaba mai dorewa na yadda zasu taimakawa makarantun da suka gaba a ciki.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply