ASUU ta yi barazanar tsunduma yajin aiki

Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’i (ASUU) ta yi barazanar tsunduma cikin wani mataki na yajin aiki sakamakon kin biyan wasu ma’aikatansu sama da 1000 albashin watanni 13.

Shugaban, kungiyar reshen jami’ar Jos, Dakta Lazarus Maigoro, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, a Jos, ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta kuma hana biyan mambobin da abin ya shafa.

Ya zargi Akanta Janar na Tarayya (AGF), Ahmed Idris kan hana malaman makarantar albashinsu, koda bayan gwamnati da kungiyar sun cimma matsaya kan kin cin zarafin mambobinta bayan yajin aikin da suka yi na karshe.

Shugaban ya yi zargin cewa ana yi wa mambobin da abin ya shafa barazanar ko dai su shiga cikin tsarin hadahadar biyan albashi da bayanan ma’aikata (IPPIS), ko kuma a dakatar da biyan albashin.

Ya bayyana cewa duk da umarnin da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar, cewa a biya mambobin kungiyar cikakken albashinsu, Akantan na kasa ya hana mambobin kungiyar da abin ya shafa albashinsu, wanda hakan ya saba wa ka’idojin yarjejeniyar da kungiyar da gwamnati suka sanya wa hannu.

Maigoro ya ce ofishin akantan na kasa ya ci gaba da ciyar da jama’a da wasu bangarorin gwamnati da dalilai na karya kan lamarin, kamar lambobin BVN da ba daidai ba, sunayen da ba daidai ba da yadda aka tsara su, da sauransu.