Asusun Tallafawa Wayanda Iftila;In Ya Shafa Ya Bayar Da Gudummawar Rigiyoyin Burtsatse Masu Amfani Da Haskan Rana Ga Makarantu.

VSF
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Asusun tallafawa wadanda iftilain ya shafa VSF a kan COVID-19 ya bayar da gudummawar rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana da sauran kayayyakin kiwon lafiya na sama da naira miliyan dari biyu da hamsin ga makarantun sakandare uku a jihohi 17 ciki harda birnin taraiya a matsayin wani bangare na matakan kariya domin magance yaduwar Corona kara na biyu a cikin ƙasar.
Shugabar kungiyar Misis Toyosi Kerele-Ogunsiji ce ta bayyana haka yayin mika kayayyakin ga Ministan Babban Birnin Tarayya Malam Musa Bello a Abuja.
Misis Ogunsiji ta bayyana cewa shirin bada agajin gaggawa na daga cikin ayyukan kungiyar ta hanyar shugaban kwamitin Laftanar Janar Thiophilus Danjuma.
A cewar ta, manufar ita ce samar da taimako ga ‘yan Najeriya a kokarin da gwamnatoci ke yi na dakile COVID-19 a jihohi 18 na tarayyar.
Da yake karbar kayayyakin, Ministan Babban Birnin Tarayya, Malam Musa Bello wanda ya samu wakilcin Mukaddashin Sakataren Ilimi na na Tarayya, Malam Abulrazak Onivoho ya yabawa kungiyar gamai da wannan taimako da suka basu , sannan ya bukaci yan Nijeriya da su dauki ilimi da mahammanci a kasar a matsayin wani nauyi da ya rataya a wuyansu.
Shugabar, Makarantar Sakandaren Governent dake Bwari, Mrs Favour Edem-Nse ta baiyana jin dadin ta da wannan tallafawa inda ta tabbatar da cewa zasuyi ammfani da kayayakan yanda ya kamata
Edem ta kuma bukaci sauran kungiyoyin hadin kai da mutane masu kyakkyawar manufa su yi koyi da kyakkyawar aikin kungiyar .

Kayayyakin da kungiyar ta bayar akan COVID-19 ga makarantu uku a dake birnin taraiya sun hada da; rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana, Wajen Wankin Hannu , takunkumin fuska guda 2000, da sauransu.

A wani lamari makamancin wannan, Asusun Tallafawa Wadanda iftila Ya Shafa, ta kuma bayar da gudummawar rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana guda uku ga makarantun sakandare uku na jihar ta Borno a wani bangare na kokarin dakile yaduwar cutar ta COVID-19 karo na biyu.

Makarantun sakandaren sune, Government College, da Arabic Teachers collage da ‘ Government Girls Secondary School Yerwa .

A yayin bikin kaddamarwar da kuma mika kyautar, Shugaban Gidauniyar, Janar Theophilus Danjuma wanda ya samu wakilcin Shugaban kungiyar COVID-19 Taskforce na Asusun Tallafawa Wadanda aftila;in ya shafa, Misis Toyosi Akerele-Ogunsiji ta ce wannan wani bangare na yaki da cutar a kasar .

Ta kara da cewa ingantacen ruwa sha , da tsaftar muhalli da tsafta makarantu zai taimaka matuka wajen macance cutar karo na biyu.

Kwamishinan Ilimi na jihar Borno, Alhaji Bello Ayuba ya ce makarantun uku sun dauki nauyin wasu makarantun sakandare 25 da rikicin ya rutsa da su wadanda ke dauke da dalibai sama da dubu goma.
Alhaji Ayuba ya ce rijiyoyin burtsatsen za su taimaka matuka wajen inganta yanayin ruwa da tsaftar muhallinsu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply