Asusun Tallafawa Wayanda iftila’I Ya Shafa, Ta Ware Naira Biliyan 3.3 Domin Shirin COVID-19

nema-officials-thumb
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Asusun tallafawa wayanda aftila,i ya shafa, sun baiyana cewa sun ware kimanin naira biliyan 3.3 domin ayyukan COVID-19 da za a yi amfani da su ma marasa galihu a kasar.

Shugabar, Kwamitin tallafawa wayanda iftila;in ya shafa a kan COVID-19, Misis Tosoyi Akerele-Ogunsuji, ta baiyana hakan yayin gabatar da gudummawar kayayyakin abinci da kayan kiwon lafiya ga Gwamnatin jihar Kano.

Akerele tace sun kashe naira biliyan 1.8 a kashin farko shirin COVID-19 ta hanyar samar da abinci da sauran kayan taimako, inda ta kara da cewa an kashe naira miliyan 832 a karkashin shirin kashi na biyu .

Ta kara da cewa ana sa ran kashe kimanin naira biliyan 1.3 a shirin , kashi na uku , wanda zai kare a watan Disamba.
haka zalika ta ce asusun zuwa yanzu ta bayar da tallafi ga jihohi 16 cikin 30 da aka Ambato a cikin shirin.
A yayin da yake jawabi Gwamna jihar kano Abdullahi umar Ganduje ya yabawa asusun tallafawa, yana mai cewa, gudummawar zai taimaka matuka wajen magance wahalhalun da mutane suke fuskanta a annobar corona .

Ganduje, wanda ya sami wakilcin Dr Ibrahim Tsanyawa, Kwamishinan Lafiya na jihar, ya ce gwamnati ta rarraba kayan tallafi na COVID-19 ga gidaje sama da 300,000 a jihar, tun lokacin da cutar ta barke a kasar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply