Asusun Kididdiga Na Majalisar Dinkin Duniya Ta Bada Gudumawar Kayan Kariya Ga Asibitoci 32 A Jihar Borno

un-2
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Asusun kididdiga na majalisar dinkin duniya ta bada gudumuwar kayayyakin kariya ga cibiyoyin lafiya na matakin fari guda 32 da kuma makarantun sakandare guda goma da sauran manyan makarantun ilimi a fadin jihar Borno.

Yayin taron da aka gudanar a birnin Maiduguri, shugaban ofishin kungiyar anan Maiduguri Mr Christian Macauley yace kayayyakin zasu karfafa da kuma kare ma’iakatan lafiya da suke yakar cututtuka.

Ya kuma bada tabbacin taimako da kungiyar zatayi na tabbatar dab’a samu cikas a harkar lafiyar yan adam cikin bazuwar annobar Covid-19 karo na biyu ba, tare da cewa kayayyakin zasu kuma taimaka wajen kai dauki ga wadanda akaci zarafin su a yankuna da suke da wahalan shiga.

Daraktan sashen aiki na ma’aikatar lafiya na jihar Borno Dr Buba Mshelia, ya bayyana cewa gudumawar zai taimaka matuka wajen magance matsalolin da harkar lafiyar ke fuskanta.

Ababen da akayi rabiyar sun hada da takunkumin fuska dubu 6, safar hannu dubu 6 da sauran su.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply