Anyi Kira Ga Gwamnatin Tarraya Da Ta Kara Kaimi Wajen Yaki Da Yan Boko haram.

borno
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar kibaku Area Development, karkashin karamar hukumar cibok a jihar Borno sunyi kira ga gwamnatin tarraya da ta kara kaimi wajen kokari da takeyi a yaki da yan kungiyar Boko haram.

Shugaban yada labarai na kungiyar Allen Manasseh shine ya bayyana hakkan a cikin wata sanarwa.

Karamar hukumar ta karade duniya ne a lokacin da yan ta’adda suka kwashi yaran makaranta su dari biyu da saba’in da shida a shekarrar dubu biyu da sha hudu.
Tun daga wannan lokaci jama’ar garin basu sake samun kwanciyar hankali ba sakamakon yawan harin da yan ta’addan suke kai musu duk dama akwai sojoji.

Da hakkan kungiyar tayi kira ga shugaban kasa da ta shawo kan matsalar tare da samar da mafita ga jama’r garin dama Arewacin kasar Baki daya.

Kungiyar tayi tuni da cewar har yanzu bata ji komai ba a game da sauran yaran makaranta dari da goma sha biyu dake hannun yan ta’adan ba.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply