Anyi kira Da A Dakatar Da Gwamnoni Daga Daukan Bashi Kudi Naira Trilliyan Goma Sha Bakwai Daga Asusun Pensho.

pension_550052083
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiya mai fafutukar bunkasa democradiya da yaki da cin hanci da rashawa sun yi buddadiyar wasika ga shugaba Muhammadu Buhari tare da kiransa da yayi amfani da kujerranshi ya gaggauta baiwa darakta janar na hukumar pensho umarnin dakatar gwamnoni daga daukan bashi zunzurutun kudi naira trilliyan goma sha bakwai daga asusun pensho.

An bayyana cewa Gwamnonin a wancan santi sun bayyana niyarsu na daukan bashin kudi naira trillion 17 daga hukuma mai lura da assusun fensho ta kasa bayan tattaunawa da sukayi da Gwamnnan kaduna Mallam Nasir el-Rufai wanda shine shugaban kwamitin shugaban kasa kan tsare-tsaren bunkasa tattalin arzikin kasar.

A cikin wata wasika da mataimakin shugaban hukumar Kolawole Oluwadare, ya sanyawa hannu yace barin gwamnoni su dauki bashin zai kawo matsala ga ma’ikata da suka dade suna aiki .

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply