Ana Samun Yaduwar Cutar Tarin Fuka A Najeriya

Darakta ta kasa kan tarin fuka da cutar kuturta Misis Idara Uko ta ce an kiyasta mutane 157,000 sun mutu daga cutar tarin fuka, yayin da yaduwar cutar da alamominta ke ci gaba dayaduwa.

Uko ta gabatar da hakan ne ranar Talata a taron horar da ‘yan jaridu na ma’aikatan lafiya na Jihohi da masu bada rahoto kan tarin fuka a Cibiyar Gaggawa dake , Maiduguri.

A cewarta, tarin fuka cuta ce da ake shaka wadda kwayar cutar ke haifarwa; kuma tana shafar huhu da sauran sassan jiki.

Ta kuma ce cutar tarin fuka ita na daya daga cikin manyan cututtukan 10 da ke haddasa mutuwa a duniya.

Aa rahoton WHO na shekarar 2020 ya bayyana Najeriya a matsayin kasa ta farko a Afirka sannan ta 6 a duniya a cikin kasashe 30 masu fama da matsalar.

Yayin da take kokawa game da karuwar cutar tarin fuka, Uko ta ce: “Najeriya ma tana cikin jerin kasashe 14 masu dauke da tarin tarin fuka cikin kasashe 30 masu alaka da cutar.

A cewar ta, cikin kashi 31 ko 138,573 masu dauke da cutar ta tarin fuka an dauki rahotanninsu a shekarar 2020, kuma kashi 69 a cikin al’ummomar basa karbar magani balle a dauki rahotanninsu daga hukumomi.

Ta kuma bayyana cewa cutar tarin fuka tana iya warkewa idan aka gano ta kuma aka kula da ita da wuri ta hanyar kiran wannan lambar 3340 kyauta.