Ana Samun Karuwar Mata Masu Dauke Da Cutar Daji Ta Nono A Najeriya – Minista

images (2)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Dr Osagie Ehanire Ministan lafiya ya nuna damuwarsa ta yadda ake samun karuwar cutar daji ta nono a fadin kasar inda yace ya kamata mata su dinga zuwa ana duba su.

Ehanire ya bayyana hakan yayin ranar cutar dajin ta duniya da aka gudanar a cibiyar dake Abuja.

Yace rahoton da cibiyar ta gudanar ya nuna cewa ana samun karuwar cutar a kasar daga shekarar 1960 zuwa 2016.

Haka nan yace tsakanin 1960 zuwa 1969 an samu Karin kashi 13.7 cikin 100 ,na mata masu dauke da cutar ta dajin Nono a najeriya.

San nan ya karu atsakanin shekarar 1990 zuwa 1999 da kashi 24.7 cikin dari na matan.

Haka nan yace tsakanin 2000 zuwa 2016 an samu Karin kashi 26.1 cikin 100 na matan dake dauke da cutar.

Inda yace wan nan ya nuna cewa cutar na karuwa a kasar kuma ya kamata ma’aikatan kiwon lafiya su duba abun.

San nan ya yabawa kungiya mai zaman kanta ta Clinton Health Access Initiative da kungiyar lafiya ta duniya wato WHO kan taimakaon Najeriyar da kayan aiki.

A nata jawabin ministar harkokin mata Mrs Pauline Tallen tace ma’aikatar ta zata cigaba da ayyukan wayar da kan mata kan cutar kuma zata yi aiki da masu ruw ad a tsaki da hukumomin da abun ya shafa don yaki da cutar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply