Ana Cigaba Da Samun Rikici A Kasar Chadi Bayan Nadin Dan Marigayi Deby

Yan siyasan adawa a Chadi sun yi watsi da nadin da sojoji suka yi wa dan tsohon shugaban kasar Idriss Déby sakamakon mutuwar mahifin nasa.

Déby, mai shekaru 68 wanda ya kwashe shekaru 30 a kan karagar mulki ya mutu bayan da aka harbe shi yayin da yake fada da ‘yan tawaye a fagen daga.
‘Yan tawayen sun kuma nuna adawa ga matakin, inda suke cewa:“ Chadi ba masarauta ba ce.

Mahamat Idriss Déby Itno, wanda aka fi sani da “Janar Kaka”, ya kasance mai kula da masu tsaron fadar shugaban kasa kuma shi ne zai jagoranci kasar tsawon watanni 18 har zuwa lokacin da za a yi zabe.

Masana sun shaidawa manema labarai cewa matakin ya sabawa kundin tsarin mulki, kuma ya kamata kakakin majalisar ya karbi mulki lokacin da shugaban da ke kan kujerar ya mutu kafin shirya zabe.

An sanar da rasuwar Déby ne a gidan Talabijin din kasar a ranar Talata kwana guda bayan sakamakon zaben na wucin gadi da aka yi hasashen zai ci wa’adi na shida a kan kujerar shugabancin kasar mai tarin arzikin mai.

An rusa gwamnati da majalisar dokoki. An kuma sanya dokar hana fita kuma an rufe iyakokin kasar ta Chadi.