An zargi Masauratar Kano Da Kokarin Maida Filin Sallah Eid, Gidajen Jama’a

KANO
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Al’ummar Darmanawa dake karamar hukumar Tarauni a jihar kano ta zargi masauratar kano da kokarin maida filin Eid dasuke sallah shekara da shekaru zuwa filaye domin ginene.

Mai magana da yawun al’ummar Tijjani Yahaya ne ya bayyanawa manema labarai haka.
Yace filin sallar gurine wanda marigayi Ado Bayero ya basu domin amfanin al’umma.

A bayanin Tijjani Yahaya , yace sarkin yasa a binciko maganar kuma sun zauna da sarkin shanun kano dakuma makaman kano Abdullahi Ibrahim.

Tijjani yace akwai fadi tashi akan maganar tun nuwamba 2020 wajen ganin an samu maslaha akan maganar.

Ya kara dacewa sun kai maganar gun hukumar yaki da cin hanci da rashawa da shaidar girman filin da kuma a matsayin filin na gurin amfanin al’umma anman hukumar tace musu filin na masauratar kano ne.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply