
Shugaban jam’iyyar PDP Mai ritaya kanal Kefas Dantala Agbu ya bukaci shugabannnin jam’iyyar dasuyi aiki kan kudurin jam’iyyar da kuma jihar.
Shugaban ya bayyana hakan yayin bikin kaddamar da kwamitin jam’iyyar na duba ayyuka a yankunan da mazabun jihar a sakatariyar jam’iyyar a Jalingo.
Haka nan yace a yanzu rayuwar yan jihar na hannun shugabannnin inda ya kamata suyi abinda ya dace ga mutanen jihar don zaba musu wadanda suka dace wanda zaisa su lashe zabubbukan.

Agbu ya godewa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar kan taimakon da suke bayarwa da kuma cigaban jam’iyyar.
Yayin da take jawabi a madadin yan kwamitin tsohuwar ministar harkokin mata hajiya Aisha Jumai Alhassan ta godewa shugaban jam’iyyar da karbar su cikin jam’iyyar kuma zasuyi aiki yadda ya dace a cikin jam’iyyar.
