An Yankewa wasu Sojoji Hukuncin A Jihar Borno

DHQ TROOPS
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Wata kotun sojoji dake zaman ta a Maiduguri ta yanke wa wani mai suna Azunna Maduabuchi hukuncin kisa sakamakon kashe wani soja na gaba dashi laftanar Babakaka Ngorgi da yayi.

Maduabuchi wanda ake tuhumar sa da kisan laftanar Ngorgi a watan Yulin shekarar 2020 a karamar hukumar Bama.

A ranar Talata ne kotu dake zaman ta a barikin Maimalari anan Maiduguri ta yanke masa hukuncin kisa bayan samun sa da laifin kashe shugaban sa.

Wasu sojojin kuma da aka kamasu da laifin kisa suma an yanke musu hukuncin shekaru da dama a gidan kaso.

Sojojin sune Sajant Sani Ishaya wanda aka yanke masa hukuncin shekaru 4 a gidan yari, sai Bidemi Fabiyi wanda aka yanke masa hukuncin shekaru 2, sai kuma Musa Bala da Abdulrasheed Adamu da aka yanke musu daurin shekaru dai daya.

Sai kuma Muhammad Kuru wanda aka yanke masa hukuncin shekaru 3 sakamakon kashe wani yaro dan shekara 12 a wajen biki, sai kuma Aja Emmanuel wanda aka rage masa mukami.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply