An Yanke Wa Wasu Mutane Fudu Hukuncin Shekaru 12 A Gidan Kaso

borno-state-small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Babban kotun jihar Borno ta yanke hukuncin shekaru 12 a gidan kaso ga mutane 4 da aka same su da laifin kisan kai.
Wannan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da aka sanyawa hannu ta hannun DCR Sadiq Dunoma a ranar 7 ga watan nan.

Sanarwar ta bayyana cewa mai shari’a Alkali Gana Wakil ya yanke hukunci wa Usman Adamu, Babagana Musa, Umar Isma’il da kuma Nura Muhammad kan laifuffuka daban daban.

Mai shari’a Wakil ya bayyana cewa yan masu laifin sun aikata ta’addanci a watan Ramadana 11 ga watan Mayu inda suka hada kungiyar mai mutane 17 wanda Itado ke jagoranta dauke da wukake da adda inda suka kai hari London Ciki, Kwanan Yobe tare da jikkata mazauna yankin kuma suka kasha Muhammad Walasta.

Daga karshe yayi kira ga gwamnatin jihar nan musamman ma ma’aikatar dake da hakkin jin dadin jama’a da ta sanya ido kan al’amuran wadan nan kungiyar in ba haka ba zasu iya canzawa zuwa kungiyar asiri domin samun kwanciya hankali a birnin Maiduguri.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply