Hukumar NDLEA Ta Wayar Da mutane Illar Shan kwayoyi da fataucin mutane.

ndlea large
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kwamandan hukumar ta ammali da miyagun kwayoyi wato NDLEA a jihar Imo, Nse Inam, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Owerri cewa a shekarar 2020, rundunar ta yi nasarori a fannoni daban-daban wajen gudanar da ayyukan su, duk da cewa an dan samu raguwa kadan daga na shekarar 2019.

Inam ya ce rundunar ta yi nasaran cafke mutane 165, wadanda suka hada da maza 145 da mata 20. ya kara da cewa matasa tsakanin shekaru 17 zuwa 35 su ne suka fi yawa a cikin wadanda aka kama.

Hakanan, rundunar ta cafke kilogram 959.677 na miyagun kwayoyi kamar su tabar wiwi ,hodar iblis, tramadol, dadai sauransu.

A cewarsa, rundunar ta wayar da kan mutane akalla 3,444 akan shaye-shayen miyagun kwayoyi da kuma hanyoyin magance matsalar a cikin al’umma.

Yakara da cewa rundunar ta shirya horar da dalibai 2,700 na Kwalejin Fasaha ta Tarayya dake Nekede,a Owerri da kuma Makarantar Sakandare Yan mata, ta Ifakala; da kuma Makarantar Sakandare Soja, na Obinze.

Rundunar ta kuma wayar da kan mutane 674 mazauna kananan hukumomin jihar
A Karshe Inam ya jaddada kudirin hukumar na cin zarafin muggan kwayoyi da fataucin mutane.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply