An Tafi Da Fasinjoji Da Dama A Titin Damaturu zuwa Maiduguri

boko-haram-group-writes-european-union-over-conduct-of-french-countries-around-lake-chad
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Yan kungiyar Boko Haram sunyi garkuwa da matafiya da dama a hanyar titin Damaturu zuwa Maiduguri.

Acewar majiyar tamu yan kungiyar ta Boko Haram sun kaiwa matafiya hari a a dai-dai garin Garin-Kuturu dake kusa da Auno a karamar hukumar Konduga da misalign karfe 1:30.

Yan ta’addan sun fito da kayan sojoji bayan sun kafa shingen bincike da motocin Hilux 5 inda suka tafi da matafiyan.

Haka nan majiyar tace sun kone wasu motoci 2 da mota kirar Volkswagen Golfda fijo.

Wata data lamarin da idonta Haijya Mairo wadda tace itama ta tsalllake rijiya da baya ta bayyanawa gidan radiyon DANDAL Kura Radio International cewa suna kusa da inda abun ya faru wanda bayan jin karararraki direban su ya juya ya koma zuwa Benisheik n.

Ta kara da cewa Jami’an sojin sun fafata day an kungiyar na Boko Haram kimanin awa daya inda bayan nan jami’an sojin suka dawo inda mutane suke sukace su biyo su inda har suka iso inda abun ya faru suka iske motocin 2 na cin wuta.

Haka nan tace sunga wata motar a daji da kuma ganin takalma da yan kwalaye na mata a kasa.

Wani jami’in tsaro ya tabbatar mana da faruwar lamarin amma yace jami’an nasu sun dakile wani hari ne da aka kai musu a babban titin wanda shiyasa mutane suka tsorata a titin na Maiduguri zuwa Damaturu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply