An Samu Sabbin Masu Dauke Da Cutar Covid19 Sama Da Dari Uku A Najeriya

corona vaccine
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar yaki da cuttutuka masu bazuwa ta kasa tace an samu mutane wadan da suka kamu da cutar covid19 su dari uku da sha takwas a cikin kasar wanda wanda duka duka ya kawo ga mutane dubu sittin da shida da da tara da dari biyu da hamsin da biyar cikin kasar baki daya.

Wakilinmu mai sa ido akan shafukan yada zumuta yace Hukumar ta bayyana hakkan ne a shafinsu na Twitter a ranar lahadi.
Hukumar sun ce mutane dari da sha ukun sun kamu ne a ranar shida ga watan December cikin shekarrar 2020.

An samu cuttutukan ne cikin jihohi goma sha hudu wanda ya hada da jihar Lagos 104, Kaduna 59, babban birnin tarraya 50, Rivers 17, Ogun 16, Kano 14, Nasarawa 14, Akwa Ibom 10, Katsina 10, Edo 7, Oyo 5, Sokoto 5, Plateau 4, sai kuma Taraba 3.

Tun daga farkon bullowar cutan zuwa yanzu an samu mutane 69,255, da suka kamu da shi inda mutane 64,774 suka warke, mutane 1,180 kuma suka rasa rayukansu cikin jihohi talatin da shida da ma birnin tarraya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply