An Samu Sabbin Masu Dauke Da Cutar Covid19, 999 A Najeriya

NCDC 3
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasa ta bayyana cewa kasar nan ta samu karin sabbin masu dauke da cutar corona da suka kai dari 9 da 99 wanda ya kama adadin su a yanzu dubu 79 da dari 7 da 89.

Cibiyar ta bayyana cewa babban birnin tarayya tana da mutane dari 4 da 16 sai jihar Legas da take da dari 3 da 24, jihar Kaduna 68, jihar Plateau 42, Kwara 32, Kano 24, Gombe14, da kuma jihohin Sokoto da Yobe da suke da mutane 12 kowannen su.

Sauran sun hada da jihar Akwa Ibom-11, Bayelsa-10, jihohin Rivers da Bauchi suna da mutane 7 kowannen su, Ogun-6, Oyo-5, jihohin Edo da Taraba suna da mutane 4 kowannen su, sai kuma jihar Jigawa 1.

A yanzu adadin masu cutar ya kai dubu 79 da dari 7 da 89, an salami mutane dubu 68 da dari 8 da 79 sannan mutane dubu 1 da dari 2 da 31 sun rigamu gidan gaskiya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply