An Samu Rahotonin Fyade Sama Da 150 A Jihar Gombe

gombe small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar yan sandan jihar Gombe tace ta samu rahotanni sama da dari 2 da 50 kan fyade a wannan shekara a fadin jihar.
Kwamishinan yan sandan jihar Maikudi Shehu shi ya bayyanawa manema labarai hakan a Gombe.

Yace duk da ana daukan mataki kan irin wanann matsalar amma fyade ga yara yana yawaita a jihar.

Yace an gurfanar da sama da wadanda ake zargi da aikata hakan a gaban kotu kuma yawancin masu aikata irin wannan hali masu shekaru sama da 50 ne inda suke lalata rayuwar yara tsakanin shekaru 3 zuwa 6.

Ya kara dacewa rundunar ta samu rahoto kusan 10 kan maza masu neman jinsin su tsakanin watan Yuni da Disamba.
Yayi kira ga iyaye dasu sanar da ire iren abubuwan nan, kuma su kai yaran zuwa asibiti domin samun cikakken kulawa.

Kuma yayi kira ga malaman addinai da na al’umma das u dinga fadakarwa jama’a kai kan illan fyade a wuraren ibada.

Daga karshe ya tabbatarwa jama’a cewa yan sanda zasu basu kariya na rayukan su da dukiyoyin su musamman a wannan lokaci na bikin kirismeti kuma yayi kira ga jama’a das u taimakawa yan sanda da bayanai domin kawar da ayyukan ta’addanci.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply