
Cibiyar yaki da cututtuka ta kasa wato NCDC ta bayyana a shafinta na Twitter tace ansamu karuwa mutane 575 masu dauke da cutar Coronavirus.
Jihar Legas ce cibiyar cutar wadda take da mutane 123 sai 100 a Abuja. Sai jihohin Delta mai 58; Edo, 52; Ogun, 42; Katsina, 24; Bayelsa, 23; Rivers, 22; Borno, 19; Plateau, 18; Ondo, 18; Oyo, 17; Kwara, 15; and Osun, 13, Enugu, 9; Nasarawa, 7; Abia, 6; Cross River, 5; Kaduna, 3; and Ekiti-1.
A najeriya yanzu ana da mutane 29,286 masu dauke da cutar ta COVID-19 inda mutane 654 suka rasa rayukansu sai 11,828 da suka warke aka sallame su.

