An Samu Karuwar Mutane 389 Masu Dauke Da Cutar Coronavirus A Najeriya

NCDC 3
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa na kasa wato NCDC ta bayyana karuwar mutane 389 masu dauke da cutar Coronavirus a shafinta na Twitter ranar Asabar.

Cibiyar tace a yanzu kasar na da mutane masu dake da COVID-19 12, 233 bayan da aka gwada mutane 74,999. Haka nan tace jiihohi 22 ne aka samu karuwar ciki harda babban birnin tarayya Abuja. Jihohin sune Lagos wadda tafi kowace jiha nada mutane 66 sai Abuja dake bi mata da mutane 50.

Ragowar sune Delta-32, Oyo-31, Borno 26, Rivers-24, Edo-23, Ebonyi-23, Anambra-17, Gombe-17, Nasarawa-14, Imo-12, Kano-12, Sokoto-12, Jigawa-8, Ogun-7, Bauchi-5, Kebbi-2, Kaduna-2 Katsina-2, Ondo-2, Abia and Niger 1.

Dandal Kura Radio International ta gano cewa mutane 3,826 sun warke sai kuma 342 da suka rasa rayukansu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply