
Hukumar hana bazuwar cututtuka na Najeriya NCDC ta sanar da an samu mutane 1,340 da suka harbu da cutar COVID-19 a Najeriya kuma 14 suka rigamu gidan gaskiya a jiya Alhamisa.
Hakan yakawo adadin wadanda suka rasu sakamakon cutar zuwa 1,632 tun bayan barkewar ta a ranar 27 ga watan fabrairu shekarar 2020.
A wannan karo Abuja itace kan gaba wajen wadanda suka harbu da cutar inda mutane 320 suka harbu d ita, sai mai bi mata jihar Lagos mai mutane 275Rivers-117, Oyo-100, Akwa Ibom-57, Ogun-51, Ebonyi-48, Benue-44, Adamawa-42, Imo-38, Kwara-35, Gombe-32, Kaduna-31, Edo-29, Osun-29 and Kano-24.

Sai kuma jihar Ekiti-15, Katsina-14, Delta-13, Nasarawa-13, Jigawa-10 and Sokoto-3.
