An Samu Asaran Rayuka Da Dama A Kasar Kamaru

cameroon
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By:Babagana Bukar Wakil, Maiduguri

A satin da ya gabata an samu asaran rayuka da dama a kasar Kamaru bayan da aka fafata tsakanin yan aware da jami’an tsaron kasar.

An kasha sojoji 4 da yan jarida 1 ranar Lahadi yayin da suka kai wasu jami’an tsaron sashin Momo dake arewa maso yammacin kasar.

Har yanzu dai ba a gano sojojin 4 da aka kasha ba amma an gano yar jaridan da aka kasha mai suna Rebecca Liwusi Jeme.

Sun rasa rayukan su ne yayin da suka taka wani abin fashewa, kuma ana zargin an yan aware ne suka dasa abin fashewar.

Haka nan a iyaka tsakanin arewa maso yamma da kuma yammacin kasar an kasha wani jami’an tsaro 2 da farin kaya 1 bayan da yan aware suka kai hari shingen jami’an tsaro dake kan babban titin Babadjou zuwa Matazem.

Haka kuma an jiwa wani jami’in tsaro da kuma direban babban mota da suke aiki a wani kamfani.
Sa’annan jami’an sojin kasar ta Kamaru sun lalata sansanin yan awaren dake Bulu kusa da Mundemba a kudu maso yamma inda suka kasha mayaka yan aware 14 suka samu makamai da dama.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply