
Manya manyan hukumomin kare lafiya 4 ta duniya sun bayyana samar da alluran rigakafin cutar Ebola wato Stockpile domin kiyaye bullar cutar.
Hukumomin kare lafiya 4 da suka samar da rigakafin alluran stockpile sun hada da hukumar lafiya ta duniya, hukumar UNICEF da Red Cross da kuma Médecins Sans Frontières wanda ya samu taimakon cibiyar assasa rigakafin daga Gavi.
Alluran Stockpile zai bada dama ga kasashen da suke da taimakon kungiyoyin lafiya domin tabbatar da an samu rigakafin ga jama’a don kiyaye bullarta.

An samar da alluran ne daga kamfanin Merck, Sharp da kuma Dohme Corp tare da tallafin gwamnatin kasar Amurka.
