An Sako Daliban Kankara Dari 3 da 44.

FB_IMG_1608239387544
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari yace an sako daliban makarantar gwamnati na Kankara su dari 3 da 44.

Gwamna Masari shi ya tabbatar da haka yayin da yake ganawa da manema labarai a gidan gwamnati a Katsina, yace babu kudin fansan da aka bayar kafin a sako daliban.

Yace dukkan daliban da aka sako suna cikin koshin lafiya sai dai gajiya da sukayi sakamakon tafiyar kafa da sukayi lokacin da aka kama su yace kuma an kai su asibiti domin duba lafiyar su da kuma daukar bayanan su.

Kafin a sako daliban said a gwamnati a dukkan matakai suka dinga tattaunawa tare da wadanda suka sace daliban.

Yayin zuwan na su a wani kauye kusa da jihar Zamfara da Katsina an gano daruruwan jami’an tsaro wasu cikin kayan aikin su suna sintiri a yankin.

Haka kuma akwai helicopta da jirgi mai saukar ungulu da suke ta sintiri a yankin dajin Rugu day a zaga kananan hukumomi da dama a jihohin Zamfara, Katsina da kuma wasu yanki a jihar Kaduna.

A nashi bangaren kuma shugaban makarantar Mal. Usman Abubakar ya bayyanawa manema labarai cewa tawagar sa sun iso Katsina domin ganawa da babban sakatare da sauran shuwagabanni na makarantar kimiyyar domin karbar daliban.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply