
Shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19 na jihar Borno kuma mataimakin gwamnan Alhaji Hon. Umar Usman kadafur ya raba kayan kariya daga cutar ga makarantun dake fadin jihar ta hannun ma’aikatar ilimi ta jihar.
Mataimakin gwamnan ya mika kayan inda ya bukaci ma’aikatar ta ilimi da suyi amfani da kayan yadda ya dace don kariya yayin da aka shiga juyi na biyu da ake fama da annobar don rabawa makarantun jihar.
Haka nan yace abubuwan da aka bayar sun hada da takunkumin rufe fuska 1,000, sabulun wanke hannu 5,000, sabulun wanke hannu 4,000, abun gwajin zafin jiki 100,takunkumi da ake wankewa 5,000 da sauransu.

Yayin da yake karbar kayan a madadin ma’aikatar ilimin kwamishina Hon. Bello Ayuba ya godewa mataimakin gwamnan da kwamitin baki daya.
Haka nan ya tabbatar musu cewa zasu raba kayan inda ya dace don kariya daga cutar.
