An Koka Da Karanci Masu Yaki Da Cutar Daji A Najeriya

nigeria
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

A ranar tunawa da cutar daji ta duniya an tunatar akan yadda mummunar cutar take samun kalubale a Najeriya sakamakon rashin kwararru da kumu samun yawn mutane masu dauke da cutar.

Hukumomin da abun ya shafa na fama da kalubale wajen yaki da cutar ta daji da ta addabiduniya.

Dandal Kura Radio International ta gano cewa cutar ta daji har yau tana daya daga cikin cutuka masu hatsari wadda bata da magani wadda kuma ke haddasa yawan mace mace a duniya baki daya.
Wadda har yanzu kariya da gano tad a maganinta na cike da kalubale a duniya baki daya.

Ana gudanar da ranar ta ciwon daji a kowace ranar 4 ga watan fabarairu inda ake wayar dakai kan cutar, kuma ake shawartar mutane dasu dinga zuwa a duba su da wuri don basu magani wanda hakan na rage saurin mace-macen.

Kungiyar lafiya ta duniya tace cutar daji itace cuta ta biyu dake da saurin kisan mutane a duniiya.

Haka nan tana faruwa daga tsiro wanda ke fitowa ko ya yadu cikin jikin dan adam wanda yake yaduwa wanda idan ba’a tare shi da wuri ba yana yaduwa ya zama mai wahala.

A najeriya mai yawan mutane fiye da miliyan 200 akwai mutane 115,950 masu dauke da cutar ta daji wanda 70,327 sun rasu a rahoton da kungiyar lafiya ta fitar a shekarar 2018 .

Daraktan nahiyar afirka na hukumar lafiya na duniya Matshidiso Moeti, yace cikin shekaru 20 cutar dajin ya rubanya a nahiyar yayin da asibitoci basu kamo mataki da ake bukata ba.

Mr Moeti yace ya zama dole a bada muhimmanci ga zuba jari domin riga kafin cutar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply