An kirayi jama’a dasu kasance masu godiya ga Allah madaukakin sarki

Babban limamin jami’ar Jiha, Sheikh Muhammad Abubakar Katchalla ya yin hudubar jumma’a na masallacin 303 ya bukaci al’umman musulmi dasu kasance masu godiya ga Allah madaukakin sarki tare kuma dayin riko da sunnan Ma’aiki SAW

Yace yan’adam nada karancin lokaci kuma Allah yaba da damar samun lada inda yace wadanda sukayi riko da ayyuka kyawawa da aiki da Al’qurani da Sunna to tabbas yanada lada mai yawa ranan gobe.

A don hakane Imam Katchalla ya bukaci al’umma dasu yawaita yin Sadaqatul Jariyah ga kawunan su dama ya’ya masu tarbiya da kuma ilimi wadanda zasu amfane su.