An Kaddamar Da Gangamin Rigakafin Cutar kyanda A Jihar Adamawa

adamawa-state
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Domin yakar cutar kyanda a jihar Adamawa tuni aka kaddamar da gangamin rigakafin cutar karo na biyu.

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ne ya bayyana haka yayin kaddamar da cibiyar kiwon lafiya dake Jimeta da gwamnatin jihar ta gina tare da hadin guiwar kungiya mai zaman kanta na Save one million lives.

Kaddamar da rigakafin cutar kyandan wani kokari ne na rage cututtuka sakamakon cutar a jihar Adamawa.

An aiwatar da ayyuka da dama da suka hada da gyare gyare da gine gine a cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko a fadin jihar.

An aiwatar da ayyuka 22 a karkashin gwamnati mai ci sannan ana kan gudanar da 6 a yanzu.

Gwamna Fintiri yay aba da kokarin kungiyar kiwon lafiya na samar da kayaki da taimako.

A nashi bangaren kwamishina kiwon lafiya farfesa Abdullahi Isa ya bayyana cewa kungiyar zata taimaka wajen yaki da cutar a jihar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply