
An gudanar da horo na kwana biyu ga kungiyoyi da mataimakan gwamna na musamman kan kafafen sadarwa na zamani inda aka wayar musu dakai kan yadda ake rubuta labarai, aikin jarida, aiki da kafafen sadarwa, daga sashin koyon aikin kafafen sadarwa na Maiduguri.
Gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum ne ya amince da bayar da horon bayan da babban mataimaki na musamman kan harkar yada labarai da hulda da jama’a Malam Isa Gusau ya kirkiro wanda shima ya halarci horon na kwan 2.
Bude horon ya samu halartar babban mai bawa gwamnan shawara kan harkar siyasa Babasheikh Haruna.

An gudanar da taron a dakin taro na Elkanemi Hall dake jami’ar inda aka fara daga ranar laraba 3 ga watan fabarairu zuwa 4 ga wata na shekarar nan.
An gabatar da lakcoci da gwajin abubuwan da aka koya.
Farfesa Danjuma Gambo ya gabatar da Lakca kan aikin jarida ta fannin shari’a da sauransu inda daga karshe aka basu takardun shedar kammala horon.
