An Girgadi Masu Sayar Da Man Fetur Da Iskar Gas A Jihohin Adamawa Da Taraba Da Su Bi Dokokin Kariya A Gidajen Mai.

petroleum
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By Hassan Umar Shallpella, Adamawa

An ja hankalin masu sayar da man fetur da iskar gas a jihohin Adamawa da Taraba da su tabbatar sun bi dokokin kariya a gidajen mai.

Kwanturolan sashen albarkatun man fetur dake ofishin Yola mai kula da jihohin biyu Sadiq Danjuma Ibrahim shi yayi wannan kira yayin ganawar da shuwagabannin kungiyar masu saida man fetur masu zaman kan su da na LPG da NARTO da kuma wakilan sauran kungiyoyi.

Wakilin mu a jihar Adamawa Hasan Umar Shallpela ya rawaito mane cewa daya daga cikin matakan da ake bukata ga gidajen mai shine su tabbatar sashen albarkatun man fetur ta amince da bangaren binne tankokin su domin tabbatar baya kusa da gidajen jama’a.

Ya kara dacewa iskar gas zai iya jawo asara da dama idan har ba’a mai da hankali ba.

Yace cikin makonni 2 an bada lasisi ga LPG6 kuma yay aba da shugabancin IPMAN na rawar da ta taka wajen tabbatar da mambobin ta bi dukkan dokoki.

A nasu jawabin shugaban kungiyar masu saida man fetur masu zaman kan su na jihohin Adamawa da Taraba Alh. Dahiru Buba, shugaban kungiyar NARTO Alh.

Auwal Ibrahim sai kuma shugaban kungiyar LPG na Yola Ibrahim Jada sun yaba wa kwanturola na sashen albarkatun man fetur bisa shugabancin sa.
COV/HUS/BBW

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply