
Najeriya ta farabada lambobin yan kasa ga yan Najeriyar r dake kasashe 16 a fadin duniya. Darakta Janaral na hukumar Mr Aliyu Aziz ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Abuja yayin da yake ganawa da masu tacewar kan yadda ya kamata a gudanar da ayyukan.
Aziz yace a watan Maris na wan nan shekarar an bawa yan Najeriyar dake kasashen Amurka, Ingila, China, Africa ta kudu, Austria, Germany da India Lambobinsu.
Haka nan yace an bawa wadanda ke kasashen Ireland, Saudi Arabia, Senegal, Togo, Canada, Benin Republic, Italy, Ghana da kashen gamayyar Larabawa.

San nan shugaban hukumar yace an tantance lambobin banki miliyan 11 inda nan gaba za’ayi na miliyan 25 million BVN a zango na biyu na wan nan shekarar.
Aziz yace mutane miliyan 41.5 da wadanda suke zaune bisa ka’ida aka bawa Lambobin tunda aka fara tantancewa a shekarar 2012.
Haka nan yace mutane miliyan 12 akayiwa rigista a yan shekaru 40 zuwa 59 years. Aziz yace sun hada kai da manema labarai don wayar da kan jama’a kan amfanin rigistar lambar.
